Wani bene mai hawa 20 ya ruguje a garin Ikoyi na jihar Legas inda mutane da dama suka makale a cikin sa.
Ginin da ake kan ginawa ya ruguje ne a titin Gerald da ke unguwar highbrow na jihar Legas.
Jami’an ceto daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), da motar daukar marasa lafiya ta Jihar, Hukumar kashe gobara, da dai sauransu sun isa yankin da lamarin ya faru domin gudanar da aikin ceto
Darakta-Janar na Hukumar LASEMA, Femi Oke-Osanyintolu, ya ce an tsara fara aikin ceton ne, bayan kiran gaggawa da hukumar ta samu.
A kwai Karin bayani……
A wani labarin Kuma na daban.
Kasar Iran ta sake nanata kudurinta cewa shirinta na nukiliya ya kasance na lumana ne a yau litinin, kwanaki biyu bayan da Amurka da Birtaniya da Faransa da kasar Jamus suka nuna matukar damuwarsu dangane da batun kera makami mai lunzami a taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Saeed Khatibzadeh ya shaidawa manema labarai a Tehran cewa, matsayin kasashen yamma basu dace da gaskiya ba kuma ba zasu kawo sakamako mai ma’ana ba.
Sanarwar da kasashen yammacin duniya suka fitar a jiya Asabar,wadda sanarwar hadin gwiwa ce bayan taron kasashen biyu da shugabanni suka yi a gefen taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a birnin Rome, ya biyo bayan tattaunawar da suka yi kan tayin Iran na ci gaba da tattaunawa kan batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015.
Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya shida na samar da mafita mai dorewa kan rikicin shirin nukiliyarta na ci gaba da tabarbarewa tun bayan da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi murabus a watan Mayun 2018 tare da kakaba mata takunkumi.
Iran ta gudanar da tattaunawar kai tsaye har guda shida a Vienna tare da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden kan komawa kan yarjejeniyar 2015, amma tattaunawar ta ci gaba da tsayawa a watan Yuni yayin da sabuwar gwamnati mai ra’ayin rikau ta fara aiki a Tehran.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanarwar da kasashen yammacin duniya suka fitar a ranar Asabar din data gabata sun bayyana kudurinsu na tabbatar da cewa Iran ba zata taba kera ko mallakar makamin nukiliya ba. ”
Sabanin bayanin, samar da karfen uranium da ingantaccen uranium, kamar yadda aka riga aka tabbatar a baya, ana gudanar da shi ne don dalilai na lumana da kuma amfanin farar hula, gami da samar da magunguna da kuma amfani da shi a matsayin mai a cikin injin bincike na Tehran, “in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Kazalika A makon daya gabata ne Iran tace zata koma tattaunawa da manyan kasashen duniya a cikin watan Nuwamba kan batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar bayan tazarar watanni 5 da aka yi ta yin gargadin cewa hakurin da kasashen duniya ke yi ya yi tsami.