A yanzu haka ‘yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Daza dake karamar hukumar Munya a jihar Neja.
Wadanda suka shaida lamarin, Kuma suka tabbatar wa jaridar Daily Trust, sun ce mazauna yankin da dama sun bar gidajensu.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa ‘yan bindiga sun mamaye al’umma da misalin karfe 5 na yamma inda suka yi garkuwa da mutane da dama.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, da kwamishinan kananan hukumomi, harkokin masarautu da na cikin gida, ba su amsa sakon da aka aike musu ba.
Sai dai wani mazaunin unguwar, Nurudeen Isyaku Daza, ya ce ‘yan bindigar na gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ba.
“Yayin da nake magana da ku, ba za mu iya tantance ainihin adadin mutanen da aka sace ba saboda ‘yan bindiga suna cikin al’umma suna gudanar da ayyukansu. Mutane da yawa sun gudu,” inji shi.
An kai wa al’ummar karamar hukumar Munya hari sau da dama a cikin makonni biyun da suka gabata.