Sa’o’I arba’in da takwas bayan sace wasu malaman makarantu uku a Christ the King Major Seminary, Fayit dake Masarautar Kagoma a karamar hukumar Jema’a, na Jihar Kaduna sun shaki iskar ‘yanci.
Rev. Fr. Emmanuel Uchechukwu Okolo, jagoran Cocin, Diocese na Kafanchan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Laraba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, “Muna son gode wa duk wadanda suka yi addu’o’i da rokon a gaggauta sakin malamanmu da sauran wadanda har yanzu suke cikin komar masu garkuwa da su.”
“Muna rokon Allah da ya gaggauta sakin wadanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da su” inji sanarwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungaza a Dimokuradiyya Martani PDP ga APC
“An umarci dukkan Malaman Majami’o da su ci gaba da Mika Godiya ga Allah a yau Alhamis 14 ga Oktoba shekarar 2021, don sakin malaman sauran wadan da suke hannun masu garkuwa da mutanen cikin sauri da aminci.”