• Rundunar sojin Sama ta kasa, ta karyata rahoton samun hadarin jirgin sama.
• Kafafen yada labarai na zamani me dai suka fara yada rahoton cewa, jirgin Saman rundunar sojin Saman ta kasa ya yi hadari a Kaduna.
• Jami’in Hulda da jama’a da bada bayanai na rundunar ne ya karyata hoton samun hadarin jirgin sama.
Rundunar sojin sama ta kasa, ta karya ta rahoton dake yawo a kafafen yada labarai na zamani cewa, daya daga cikin jirgin ta, ya yi hadari a yau lahadi.
Babban Daraktan Hulda da jama’a da bada bayanai na rundunar sojin Saman, Air Commodore Edward Gabwet ne ya mai da martani kan rahoton dake cewa, jirgin saman rundunar ya yi hadari a Kaduna, inda ya ce ” Babu wani rahoton hadarin jirgin sama a Kaduna”.
Ya kara da cewa, ya tuntubi jami’an da ke yankin, amma sun tabbatar mai da cewa, Babu wani jirgin rundunar da ya taso daga Yola babban birnin jihar Adamawa zuwa Kaduna a yau Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da duminsa: Mutum daya ya baƙunci lahira a sabon harin Kaduna
” Babu hadarin jirgi a Kaduna, kuma babu wani jirgin sama da ya tashi daga Yola zuwa Kaduna. Na sha tuntubar jami’an dake aiki a yankin, amma haryanzu babu wani abu makamancin hakan” inji shi.
Sai dai a wani labarin kuma, majiya daga rundunar sojin ta ce, da yuwuwar samun hadarin jirgin sama, amma haryanzu bayanan basu inganta ba.