Cibiyar dakile Cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar da samun rahoton cutar Omicron COVID-19 guda biyu a Najeriya.
Hukumar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Darakta Janar, Dr Ifedayo Adetifa.
NCDC ta ce an gano mutum biyu dauke da alamomin cutar na”sequencing Genomic”.
“A bisa tsarin gwajin balaguro na yau da kullun da ake buƙata na duk matafiya na ƙasashen waje da tsarin tsarin kwayoyin halitta a Cibiyar dakile Cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta hanyar amfani da dakin gwaje-gwaje ta National Reference Laboratory, Abuja, ta tabbatar da Bullard cutar Corona a Najeriya samfarin Omicron.”
“Tsarin kwayar cutar daga ranar gwaji na kwana biyu ga matafiya zuwa Najeriya ta gano wasu nau’ikan Omicron guda biyu a tsakanin matafiya daga Afirka ta Kudu da suka isa Najeriya a makon da ya gabata.”
Wannan lamari na zuwa ne ne bayan kasar Canada ta ce ta gano wasu mata biyu Yan Najeriya, dauke da Samfarin Cutar ta Omicron.
Comments 1