Yanzu-Yanzu: NECO Ta Fitar da Sakamakon Jarabawar SSCE ta 2022
Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2022 (SSSCE) da aka gudanar a fadin kasar, a cikin watan Yuli.
Magatakardar NECO kuma Babban Jami’in Hukumar, Farfesa Dantali Wushishi, a lokacin da yake zantawa da Manema Labarai a Minna, Babban Birnin Jihar Neja a ranar Alhamis, ya ce Ɗalibai 1,209,703 ne suka zana jarrabawar, inda kashi 60.74 ( 727,864) suka samu maki biyar zuwa sama da suka hada da Ingilishi da kuma Lissafi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilan da yasa Zamfara ta tsakiya bata samar da Gwamna ba tun 1999 – Jabaka
Ya ce idan aka kwatanta da 2021 SSCE na 878,925 (71.64%) da suka wuce a Turanci da Lissafi, an samu raguwar kashi 10.9 cikin 100.
A wani labarin kuma: Kwamitin Yaƙin neman Zaɓe: APC ta musanta wasikar gargaɗi da Adamu ya rubuta wa Tinubu
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce Abdullahi Adamu, shugaban kasa, bai taba rubuta wa dan takarar shugaban kasa Bola Tinubu wasikar gargadi ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, Adamu, tsohon Gwamnan Nasarawa ya koka kan yadda kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa (PCC) ya kafa.
Sanarwar da Sakataren Yada Labarai na kasa Felix Morka ya fitar a ranar Juma’a ta ce sanarwar “ba ta fito daga jam’iyyar ba.”