Hukumar Kula da Ƙungiyar Ƙwallon Najeriya ta naɗa ɗan ƙasar Portuguese Jose Peseiro a Matsayin sabon Kocin Ƙungiyar Ƙwallon ta Ƙasa wato Super Eagles.
NFF ta bayyana haka a cikin wata sanarwar bayan taro a cikin wata takarda da aka fitar a ranar Laraba, bayan taron Shuwagabanni na Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu kuɗin dake da halin sayen Makamai, Ƙwayoyi, sune ƙashin bayan matsalar tsaron Najeriya — Hamza Al-Mustapha
“Bayan yin dubi akan wata sanarwa da aka gabatar wa shugaban Karamin Ƙwamitin Ayyuka, Shuwagabannin Babban Kwamiti sun amince da naɗa Mr Jose Peseiro a matsayin sabon Kocin Super Eagles bayan rabuwa da Mr Gernot Rohr,” Inji sanarwar.