Tawagar lauyoyin da ke kare jagoran haramtacciuar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra IPOB Nnamdi Kanu, sun shigar da kara a Kenya kan gwamnatin kasar dake gabashin Nahiyar Afurika.
Mai ba Mazi Nnamsi Kanu shawara na musamman ga Aloy Ejimakor ne ya yi wannan ikirarin, ta sannan shafinsa na Twitter a safiyar yau Alhamis.
EJimakor ya wallafa cewa, “Yanzu-Yanzu: Kungiyar lauyoyin Onyendu ta shigar da kara a Kenya, kan gwamnatin Kasar ta Kenya.”
Majiyar Jaridar dimokuradiiya ta ruwaito cewa, idan za’a iya tunawa an kama Kanu ne a watan Yunin shekarar nan a kasar Kenya, Inda daga bisani a ka dawo da shi gida Nigeria.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za mu koya wa yan bindiga yaren da suke fahimta, inji Shugaban Soji
Duk da cewa babban kwamishinan kasar Kenya Wilfred Machage ya karyata ikirarin cewa, yan sandan Kenya ne suka kama Kanu, Amma masu fafutukar IPOB a ko da yaushe, suna yi wa Kenya shagube, kan hada baki da ita, wurin kama Mazi Nnamdi Kanu.
Ko da yake dai, ana sa ran Kanu zai sake gurfana a gaban kotu a watan Oktoba Mai zuwa. Ya yin da Gwamnatin Nageria ke ci gaba da tuhumar sa da laifin cin amanar kasa.
A wani labarin Kuma na daban.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban taro na 2 na musamman na hukumar shugabannin kasashe da gwamnatoci na ECOWAS kan yanayin siyasa a Jamhuriyar Guinea.
Babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ne ya bayyana hakan da safiyar yau Alhamis.
Amakon da ya gabata Osinbajo ya halarci babban taron ECOWAS na ban mamaki kan duba halin siyasar kasashen Guinea da Mali, inda aka gudanar da taron a ranar 8 ga Satumba.
Taron wanda a yanzu haka yake gudana a yau Alhamis zai sake nazarin halin da ake ciki a Kasar Guinea dangane da rahoton babban taron ECOWAS zuwa Conakry.
Mataimakin shugaban kasar, wanda zai bar Abuja da safiyar yau, zai kasance tare da karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu sannan kuma ana sa ran zai dawo Abuja daga baya a ranar Alhamis.