By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na wani dan lokaci a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon wani yanayi da ba a taba gani ba.
Ya bayyana hakan ne a safiyar ranar Talata.
DUBA WANNAN LABARIN: ‘Rashin Wayar Da Kan Jama’a Yana Haifar Da Nuna Wariya Ga Mutanen Da Tarin Fuka Ya Shafa’
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, a daren ranar Litinin ne wasu ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan da ke kan hanyar Kaduna tare da fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba hari.
Rahotanni sun bayyana cewa an sami wasu da ake zargin yan bindigane a ranar Litinin sun tayar da abun fashewa (Bom) akan titin jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna jikin wani jirgin kasa mai dauke da fasinjoji 970.
An ce ‘yan bindigar sun tarwatsa titin jirgin, lamarin da ya tilasta wa jirgin mai daukar nauyin 1000 ya karkata zuwa hanyar Rijana, wani kauye da ke kan hanyar layin dogo a Kaduna.
NRC, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na Twitter a ranar Talata, ta ce: “Ya ku fasinjoji, saboda abubuwan da ba a yi tsammani ba, an dakatar da ayyukan jirgin kasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna na wani dan lokaci.
“Za a ba da ƙarin sadarwa a kan lokaci.”