A halin yanzu mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo (SAN) yana karbar bakuncin mambobin kungiyar gwamnonin jam’iyar APC Mai mulki (PGF) zuwa buda baki a fadar sa dake Akinola Aguda House a Abuja a daren yau Lahadi.
Majiyoyin da ke kusa da ofishin mataimakin shugaban kasar sun yi nuni da cewa Farfesa Osinbajo zai yi amfani da wannan damar wajen tuntubar gwamnonin jam’iyyar APC kan kudirin sa na tsayawa Takaran shugaban kasa.
Da misalin karfe 6:45 na yamma, gwamnonin da ba su gaza shida ba, ciki har da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, da takwaransa na jihar Ogun, Dapo Abiodun, tuni suka shiga harabar gidan.
Sauran gwamnonin jam’iyyar APC da aka gansu kafin karfe 7 na yamma da aka shirya gudanar da taron sun hada da Hope Uzodinma na Imo; Babajide Sanwo-Olu na Legas da Gboyega Oyetola na Osun.
Taron wanda ya yi kama da na gwamnonin ne da aka gayyata, da wasu mukarrabansu kadai, bai Baiwa ‘yan jarida damar shigaharabar gidan mataimakin shugaban kasan ba.