Yanzu-Yanzu: Peter Obi na ganawar Sirri da Gwamnan Rivers Wike, a Gidan sa na Fatakwal
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar Labour Party Peter Obi a ranar Laraba yakai ziyara ga Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike a Gidan sa dake Fatakwal.
Da isar sa, Obi an Kai shi wurin da za’a yi taron da Gwamnan na sirri.
Haka zalika, dukkanin su dai har yanzu basu magana ba akan dalilin su na gudanar da taron, a yayinda aka hana ƴan Jarida damar shiga wurin da ake gudanar da taron.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sai ka nuna mana inda muka lalata bututun Mai a Najeriya — IPOB ga Buhari
Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike ya Kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP, inda ya samu nasarar zuwa na biyu.
Hakanan kuma, Peter Obi ya kasance Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a PDP, kafin daga bisani ya canja sheƙa zuwa Jam’iyyar Labour Party, Inda ya samu takarar shugaban kasa.