Hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ ta yi nasarar ‘yantar da mutum 10 da aka yi garkuwa da su tare da hallaka ‘yan bindiga da kuma cafke daya daga cikin ‘yan bindigar a jihohin Katsina da Zamfara.
Daraktan watsa labarai na rundunar tsaron sojin, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce sojojin sun yi nasarar ne a wurare daban-daban a ranar Alhamis.
Ya ce rundunar sojin a ranar Alhamis sun fafata da ‘yan bindigar a yayin da suka kai wani samame a daidai Gidan Dan Nunu da Dutsi dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Ya kara da cewa a Dangulbi, sun yi nasarar cafke wani mai suna Zayanu Abdullahi a yankin Shinkafi da kudade masu yawan gaske a yayin da aka tsayar da shi domin bincike. Ya ce a binciken da suka yi, sun gano cewa wanda ake zargi ya siya shanun sata ne daga ‘yan bindigar.
Haka zalika ya ce sun samu rahotanni sirri cewa ‘yan bindiga za su kai hari a kauyen Kimbisawa dake karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, inda suka yi maza suka kai dauki tare da ‘yantar da mata guda biyu da yaro daya da aka yi garkuwa da su. Ya ce tuni wadanda suka ‘yantar aka hada su da iyalansu.