Rundunar sojin ruwan Najeriya, a ranar Talata ta sanar da nadin Commodore Adedotun Olukayode Ayo-Vaughan a matsayin sabon kakakinta bayan sauya wurin aiki da tsohon kakakin nata , Commodore Suleman Dahun samu.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan tsare-tsare Rear Admiral JD Akpan, “yanzu Dahun ya zama daraktan hadin gwiwar sojojin farar hula.”
Commodore Ayo-Vaughan memba ne na kwas na 43 na Kwalejin Tsaro ta Najeriya.
Ya yi digirin farko na Kimiyya a Chemistry da Digiri na biyu a fannin Harkokin Kasa da Kasa da Diflomasiya a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ya kuma yi Digiri na biyu a sashin gudanarwa na fannin tsaro dake kasar, Faransa, inda Kuma yayi karatu a Jami’ar Texas dake kasar Amurka.
Kazalika ya halarci Kwalejin horas da dabarun Yyaƙin na (Ecole de Guerre), dake Paris, Babban birnin Faransa