Gwamnan jihar Kaduna, Ahmad Nasir El-Rufai da takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello, sun isa kotun koli domin sa ido kan shari’ar da jihohinsu ke yi da gwamnatin tarayya kan rashin issassun kudi.
Gwamnonin biyu sun isa zauren kotun ne da misalin karfe 8:30 na safe tare da mabiyansu da manyan jami’an gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Mu Bijirewa Hukuncin Kotun Koli Akan Kudin Naira Ba – Fadar Shugaban Kasa
Ana sa ran Gwamnatin Tarayya za ta yi galaba kan Jihohi uku da ke kalubalantar aiwatar da tsarin nan na Cashless Policy da Babban Bankin Najeriya ya bullo da shi.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, sama da manyan Lauyoyi 100 na Gwamnatin Tarayya da Jihohin uku suka isa kotun domin gabatar da Shaidu kan wanda suke karewa.
DAILY POST ta bayyana a cikin jerin dalilan da suka sa kotun ta ce jihar Ondo ta hada kai da jihohin uku a shari’a.
A ranar 8 ga watan Fabrairu ne kwamitin mutane bakwai karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro, ya dakatar da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a wani hukunci da wata jam’iyyar ta shigar da wasu jihohi uku na arewacin kasar nan wato Kaduna, Kogi da Zamfara.
A wani labari kuma, An Dawo Da Wasu ‘Yan Najeriya 150 Daga Jamhuriyar Nijar
Akalla ‘yan Najeriya 150 ne a jiya aka dawo da su gida daga Yamai na Jamhuriyar Nijar. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta tarbe su a filin jirgin Murtala.
Akalla ‘yan Najeriya 150 ne a jiya aka dawo da su gida daga Yamai na Jamhuriyar Nijar