A ranar Laraba ne wasu Sanatoci biyu suka bayyana ficewa daga tsoffin jam’iyyunsu na siyasa zuwa wata jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.
Sanatocin sun hada da: Francis Ezenwa Onyewusi mai wakiltar Imo ta gabas Sanata da Haliru Dauda Jika mai wakiltar Bauchi ta tsakiya.
Shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ne ya bayyana sauya shekar nasu yayin zaman majalisar a ranar Laraba.
Yayin da Sanata Francis Onyewusi wanda ya zama dan majalisar dattawa na farko dan jam’iyyar PDP ne kuma ya koma jam’iyyar Labour (LP), shi kuwa takwaransa na Bauchi ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a baya. Ya koma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Sanatocin da suka sauya sheka sun bayyana rashin adalci a tsoffin jam’iyyunsu wanda ya sanya suka fadi zaben fidda gwani.