Alhaji Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya a na jihar Kano, ya rasu.
Wata majiya ta tabbatar wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya haka a safiyar yau Laraba, amma ba ta yi cikakken Karin bayani ba.
Gaya na daya daga cikin manyan masarautu biyar na fadin jihar Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Motane 7 sun mutu yayin da Mota ta afka Kogin Niger
Marigayin shi ne Tsohon hakimin Kunchi, da na Minjibir, kafin a karamai girma zuwa sarkin Gaya a shekarar 2019.
A wani labarin Kuma na daban
Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta zartar da kasafin kudin jihar na Naira biliyan 142.72 don zama doka,Ƙarin kasafin kuɗi ya ƙunshi Naira biliyan 39.30 wanda za’a kashe na kananun ayyuka da kuma Naira biliyan 103.42 na manyan ayyuka.
Wannan ya biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Kula da Kasafin Kuɗi na Majalisar zuwa ga Shugaban Majalisar, kuma memba mai wakiltar Mazabar Ikot Abasi, Uduak Odudoh ga Majalisar yayin gudanar da zaman majalisar na ranar Talata.
Idan zaku iya tunawa a ranar Talata, 14 ga Satumba, 2021, Majalisar ta karɓi Ƙarin Kasafin Kudin daga ban garen Zartarwa, inda ta roƙe ta da ta ƙara kasafin farko na 2021 na Naira biliyan 456.3 domin ta ci gaba da aiwatar da shirye shiryenta.
“Kasafin Kudin kamar yadda Kwamishinan kudi Hon, Dr. Linus Nkang da Kwamishinan Ci gaban Tattalin Arziki, da kwamishinan tashar jirgin ruwa, Mista Akan Okon an yi hakan ne don magance tasirin hauhawar farashin kayayyaki,da haɓaka ƙimar musayar kudaden waje akan fifiko da manyan shirye shirye da ayyukan gwamnati don yin tasiri da isar da shi akan lokaci, ”in ji shi.
Dangane da haka, bayan da aka duba rahoton a Kwamitin Kayayyakin da Majalisar ta gabatar, an karanta dokar a karo na uku kuma ta samu tsallakewa inda ta zama doka.
A nasa jawabin, Kakakin majalisar, Mista Aniekan Bassey, ya umarci magatakarda, Misis Mandu Umoren da ta sanar da matakin majalisar ga bangaren zartarwa na gwamnati.kazalika majalisar ta dage zaman ta zuwa ranar Alhamis, 23 ga Satumba, 2021.
Comments 1