A cikin awanni 24 bayan kammala Mukabala tsakanin wasu Malamain addinin Musulunci na Kano, da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ya ne mi afuwan al’uma, inda ya ce, kwata-kwata ba a fahimce ikirarin da ya yi bane
Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyana haka ne a cikin wani fai-fan murya da ya saki a yau Asabar, Wanda jaridar Dimokuradiyya ta sa mu, inda ya ke cewa,” idan da ace kalaman da nayi na kashin kaina ne, Kuma ace nine na yi su, Kuma basa cikin wasu littattafan addinin Musulunci, don haka laifi ne babba Wanda ya daya dace ace na nemi afuwa”
Sheikh Kabara daya daga cikin jagororin darikar Qadiriyha a jihar Kano, sanan ne a bangaran ce-ce-ku-ce kan fannin addini, da kuma yin wasu kalamai da ake ganin su a matsayin zagi, da cin mutunci ga fiyayyan halitta Annabi Muhammadu S.A.W, da kuma sahabban shi.
A dai jiya Asabar ce, Gwamnatin jihar Kano ta shirya wani Mukabala da Sannan nan Malamain, da wasu Malaman addinin Musulunci da ke ciki da wajan jihar, domin tattauna wa a kan wasu kalaman Nasiru Kabara da yayi a wurin wa’azin shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Badaru: Buhari na bacci da Yan Naijeriya a ran su
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Ana daf da gurfanar da Abduljabbar a gaban Kotu, bisa zargin Kalaman Batanci, cin-mutunci, da kuma laifin raba kan Al’uma,
Kazalika tuni dai rundunar Yan sandan jihar ta Kano, ta aike wa Abduljabbar wata takadda, domin gurfanar a shelkwatar rundunar, a gobe Litinin.