Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganawa da shugabannin tsaro da na leken asiri a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Kodayake ba a bayar da cikakken bayani a hukumance ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton, majiyoyi sun sanar da Jaridar Dimokuradiiya cewa, sun yin bitar ci gaban tsaro na baya -bayan nan ne a fadin kasar.
Daga cikin wadanda suka halarci Taron akwai; Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi Mai ritaya, Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama, shugaban ma’aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da Mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno Mai ritaya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta Dage Sauraron Shari’ar Nnamdi Kanu
Sauran su ne Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor; Babban Hafsan Sojojin kasa Laftanar Janar Farouk Yahaya, Babban Hafsan Sojojin Ruwa Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo, Babban Hafsan Sojojin Sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao, Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya na Kasa DSS Yusuf Bichi, da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa NIA Ahmed Rufai Abubakar.
A wani labarin Kuma na daban
Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, a ranar Laraba, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 na naira biliyan 310.7 ga majalisar dokokin jihar.
“Kasafin Ci Gaban Dorewa,” Ma’aikatar Ayyuka da Ababen more rayuwa suna da mafi girman kason na Naira biliyan 51 don fitar da muhimmin shirin samar da ababen more rayuwa na gwamnatin sa.
Ma’aikatar Aikin Noma an ware mata Naira biliyan 12, sai bangaren ilimi da kiwon lafiya, wanda aka ware musu Naira biliyan 4 kowannensu, yayin da aka warewa ma’aikatar kudi Naira biliyan 3.
Sanarwar da babban sakataren yada labaran sa, ya rabawa manema labarai, yace Mista Daniel Alabrah, ya bayyana gwamnan na cewa ma’aikatun wutar lantarki, sufuri da watsa labarai, dabaru da wayar da kai sun samu naira biliyan daya da rabi kowannensu yayin da ma’aikatar gidaje da ci gaban karkara, ayyuka na musamman inda aka warewa Al’ummar Ijaw na Kasa Naira Biliyan 1 kowanne.
An tattara asusun kudaden shiga, fansho da garatuti, rukunin yankunan ci gaban karkara 32, cire kudaden tarayya, biyan bashin da sauran ragin da aka kiyasta akan Naira 61,755,267,518, wanda ke wakiltar kashi 19.88 cikin dari na jimlar kasafin.
Sanata Diri ya kuma yi karin haske game da kimar kudaden shiga na kasafin kudi tare da bude Naira biliyan 1.902, wanda ya hada da rabe -raben doka na Naira biliyan 43.034, Darajar kudin haraji 15.233, kashi 13% da aka samu Naira biliyan 117.3, danyen mai Naira biliyan 43.57, a cikin gida ya samar da kudaden shiga Naira biliyan 20 a tsakanin wasu abubuwa da kuma rancen Naira biliyan 43.57 inda akayi jimillar Naira biliyan 310.7.
Mai kula da Bayelsa yace Tsarin Kudin Matsakaicin Tsawon Shekaru na shekarar 2022-2024 ya dogara ne kan wasu mahimman hasashe, waɗanda ke samar da danyen mai a kowace rana na ganga miliyan 1.88, tsinkayen farashin mai na dalar Amurka 57 ga ganga daya akan canjin kudin najeriya Naira 410.15 zuwa dalar Amurka ɗaya.