Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin zauren majalisar don gabatar da kiyasin kasafin kudin shekarar 2022 a gaban dukkanin majalissar gwiwa ta kasar nan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya nemi a yi addu’ar bude taro na Kirista da Musulunci, kafin a ci gaba da gudanar da zaman.
A ranar Laraba ce dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da dukkan majalisun kasar nan, inda ya sanar da ‘yan majalisar cewa zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 a gaban su, da karfe 12 na ranar Alhamis.
Masana suna hasashen cewa, kasafin kudin shekarar 2022 da zai iya kai naira tiriliyan 16.39.
KARANTA WANNAN LABARIN:Oshimhe ya lashe Gwarzon Seria A na watan Satumba
A safiyar yau, an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen ginin Majalisar Dokoki ta kasa, da ke Abuja kafin taron.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, jami’an tsaro da ke kofar shiga Majalisar Dokoki na gudanar da cikakken bincike kan ma’aikatan dake Zauren, da sauran mutanen da ke shiga harabar kafin a ba su izinin shiga.
Wakilin jaridar Daily ya ce, ana hana wadanda ba su da katin iriznin wucewa, zuwa harabar Majalisar Dokoki ta kasa.