Gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da zai guna a ranar Asabar, shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu yana wata muhimmiyar ganawa da gwamnonin da aka zaba a dandalin jam’iyyar, The Nation ta rawaito.
Taron wanda aka fara da misalin karfe 2:35 na rana a dakin taro na kwamitin ayyuka na kasa NWC dake sakatariyar jam’iyyar, ya jawo hankalin gwamnonin Filato, Nasarawa, Neja, Kaduna da kuma Kogi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk Satar Da Ku Ka Yi Yanzu Ba Ta Da Amfani — Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnonin Dake Sukar Buhari
Sauran sun hada da gwamnonin Gombe, Yobe, Zamfara, Ekiti da Jigawa tare da mataimakan gwamnonin Imo da Katsina.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Adamu ya jagoranci mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar (Arewa) Sanata Aba Kiyari; Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa shiyyar (kudu) Cif Emma Enekwu da sakataren jam’iyyar na kasa, Otunba Iyiola Omisore ga taron.
Ya ce shugaban kungiyar Gwamnonin PGF da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu sun samu tsaikon tashin jirgi.
Ya yabawa Gwamnonin bisa rawar da suka taka a yakin neman zaben shugaban kasa da ke gudana.
“Na yi farin ciki da martanin da aka bayar ya zuwa yanzu kuma da fahimtar da yawa daga cikin mambobinmu da suke kan hanyarsu ta zuwa wannan taro.
“Za ku tuna abubuwan da suka faru a baya-bayan nan da suka sa ake bukatar wannan gayyatar.
“Ba mu so mu zauna a yanke hukunci ko wani game da inda muke a yau a cikin kasar kamar yadda ya shafi babbar jam’iyyarmu ba.
“Na ga abin da ya fi da cewa a yi shi ne a samu duk wadanda ke rike da madafan iko a kan mukamansu kuma wadanda aka zabe su a dandalin jam’iyyar su hadu a yi mu’amala da juna ta yadda za mu samu kyakkyawar fahimta ko kuma fahimtar juna don ganin wane hali muke ciki.
“Wannan ita ce ainihin wannan gayyata. Kuma ina farin cikin yi muku maraba da gaske ga wannan mu’amala,” inji shi.
A wani labarin kuma, El-Rufai ya umurci Ma’aikatun Kaduna da su karbi tsofaffin Kuɗi
Gwamna Nasir el-Rufai na jihar Kaduna ya umurci masu karɓar kuɗaɗen shiga na Ma’aikatu, da Hukumomi, da ke jihar da su karbi tsofaffin takardun kudi na Naira.
Umurnin El-Rufa’i ya dogara ne akan hukuncin da kotun koli ta yanke kan tsofaffin takardun naira.