By Abbas Yakubu Yaura
Emmanuel Leweh, shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa ya rasu.
Wata majiya da ta zanta da jaridar Aminiya ta ce marigayin ya gana da ’yan majalisarsa a sakatariyar da ke karamar hukumar Akwanga ta jihar a ranar Litinin.
A cewar majiyar, marigayin ya yi dirar mikiya ne a sakatariyar karamar hukumar Akwanga, jim kadan bayan kammala taron.
Leweh, wanda ya kwashe watanni uku yana mulki, an ce ya mutu ne a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja, ranar Alhamis.
Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa, Samuel Tsebe ya tabbatar da rasuwar tasa.
Kalamansa: “Na rasa babban yayana (Hon Emmanuel Joseph Leweh, shugaban zartarwa na karamar hukumar Akwanga) cikin sanyin jiki a yammacin yau bayan gajeriyar rashin lafiya.”