Shugaban kasa, MMuhammadu Buhari ya tarbi gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, a fadar gwamnati da ke Abuja ranar Laraba.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan, wanda ya yada hotuna daga taron a shafukan sada zumunta na zamani.
“Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a gidan gwamnati a ranar 13 ga Oktoba 2021,” inji FemiAdesina.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yan bindiga sun farmaki Yan sanda
Sai dai hadimin shugaban kasa ya kasa bada cikakkun bayanai kan taron.
Comments 1