Sufeta Janar na yan sandan Nigeria Usman Alkali Baba ya bada umarnin dakatar da mataimakin Kwamishinan yan sanda Abba Kyari daga rundunar yan sandan Nigeria.
Abba Kyari dai mutum ne da kowa ya aminta da shi, kama daga abokan aikinsa yan sanda da ma sauran yan Nigeria, sai a baya bayan nan ana tuhumarsa da zargin cin kuɗin haram da kasurgumin dan damfarar nan Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi.
Tun a farkon makon nan ne wata kotun shiya dake birnin California na Amurka, ta fitar da wata takarda dake nuni da cewa Hushpuppi ya yi anfani da Kyari wajen kamawa tare da hukunta wani mai suna Vincent Chibuzor.
Kamar yadda takardar kotun ta bayyana, an kama Vincent ne bayan da ya yi yunkurin fallasa wata tabargaza na damfarar wani hamshakin dan kasuwa daa kasar Qatar.
Wannan ya sa jim kaɗan bayan fitar da takardar, Sufeta Janar na yan sandan Nigeria Usman Alkali Baba ya bada umarnin fara binciken gaggawa kan Abba Kyari wanda Kotun Kasar Amurka take gudanarwa.
Sai dai yanzu haka Kakakin Rundunar Yan Sandar Najeriya Frank Mba ya fitar da wata sanarwar dakatarwar daga Sufeta Janar na yan sandan, kwanaki biyu bayan fara binciken inda Sanarwar ta ce ba za a maida Abba Kyari ba har sa abinda binciken ya tabbatar.