Yanzu-Yanzu: Tinubu ya bar Osun, zai gana da Kakakin Majalisu na Ƙasa a Abuja
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Bola Tinubu ya bar Jahar Osun inda ake cigaba da gudanar da zaben Gwamna.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano cewa Jigon Jam’iyyar APC zai gana da Shugabannin Majalisu na Kasa daga Jam’iyyar a ranar Asabar a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Osun: Adeleke na gaba Oyetola da kuri’u sama da 10,000 a shafin INEC
A lokacin taron, Tinubu yasha alwashin zai basu kula wa a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen sa gabanin Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Shuwagabannin Majalisu da suka halarci taron sun ƙunshi na Jahar Lagos Mudashiru Obasa, da Olakunke Oluomo na Jahar Ogun, da Idris Garba na Jahar Jigawa, da Kennedy Ibeh na Jahar Imo, da Etenh Williams na Jahar Cross River, da Funminiyi Afuye na Jahar Ekiti, da kuma Oleyegologun Bamidele a Jahar Ondo.
Sauran sun ƙunshi Abdulkareem Lawan na Jahar Borno, da Abdullahi Bawa Wuse na Jahar Niger, da Ahmed Lawan Mirwa na Jahar Yobe, da Musa Maigari na Jahar Katsina, da kuma Siddi Buba Mataimakin Shugaban Majalisar a Gombe.
Tinubu ya yabawa Shuwagabannin Majalisun da irin gagarumar gudummawa da suka bada wajen ganin ya zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar.
Ya bayyana dalilin daya sanya ya zabi Tsohon Gwamnan Jahar Borno, Kashim Shettima domin ya zama mataimakin sa.
Sun ziyarci Tinubu ne domin su taya shi murna akan samun nasarar da yayi a Babban Zaɓen da aka gudanar na Jam’iyyar.