Bola Tinubu, Jagoran Jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, ya dawo Najeriya a yau Juma’a, bayan ya shafe watanni yana jinya a kasashen waje.
Rahotanni suna nuna cewa, daga cikin wadanda ke filin jirgin sama na Murtala Muhammed, Legas don ganawa da Tinubu akwai gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, da wasu jiga-jigan jam’iyar APC.
Kakakin yada labarai, na Tinubu Tunde Rahman ne ya tabbatar da dawowa Jagoran Jam’iyar.
“Ina tabbatar muku da cewa Asiwaju ya sauka Nageria Lami Lafiya ”, kamar yadda ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun saki Daliban Baptist a yau Juma’a
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya shafe wasu watanni yana jinya a kasar waje, domin yin hutu da jinya.
Yayin da yake can, Ya shahara a kafafen sada zumunta don samun manyan manyan ziyarce -ziyarce ciki har da na Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.