A rikita rikitar APC a Kano, tsagin Malam Shekarau, tsohon gwamnan Kano ya zaɓi Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaban jamiyyar APC a jihar.
Zaben na su ya gudana ne a wani muhalli a Janguza dake yankin karamar hukumar Tofa kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Wannan na zuwa ne bayan da tsagin gwamna Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano.
Bayanai sun ce tuni shugabannin ɓangarorin biyu suka yi jawabin amincewa da matsayin.
Hakan ya ƙara fito da ɓaraka tsakanin ƴaƴan APC a jihar Kano, yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar zaɓen 2023.