Tsohon babban Sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan (IGP), Mustapha Balogun, wanda aka fi sani da Tafa Balogun ya rasu.
Majiyoyin iyalansa sun tabbatar da mutuwar Balogun, a daren Alhamis din nan, wanda ya zama IGP a watan Maris 2002, amma ba su yi cikakken bayani ba.
An haife shi a ranar 8 ga Agusta, 1947 a garin Ila-Orangun a Jihar Osun, Tafa Balogun, shi ne babban Sufeto janaral na ‘yan sanda na 21. Ya kasance memba na cadet Assistant Superintendent of Police Course (ASP) kwas na 3. Ya yi aiki a matsayin jami’in dan sanda daban-daban a fadin tarayya, kuma ya samu karin girma kamar yadda ya kamata, Tafa, ya kasance a lokacin, Principal Staff Officer (PSO) wato shugaban ma’aikatan jami’ai daga nan zuwa tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Muhammadu Gambo, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo, tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Delta. Ya kuma kasance CP a jihohin Ribas da Abia.
Tafa, ya halarci jami’ar soja a Najeriya, Kwalejin Yaki ta Kasa, daga baya ya zama Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda A.I.G shiyya ta daya, Kano, inda daga nan ne aka nada shi IGP na 21 a ranar 6 ga Maris, 2002.
Wata Shari’ar da ta ja hankalin duniya a shekarar 2005. A ranar 4 ga watan Afrilu, 2005, Tafa Balogun ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa laifin sata da kuma karkatar da sama da dala miliyan 100 a cikin shekaru uku da ya yi a matsayin babban Sufeto Janar na ‘yan sanda daga asusun ‘yan sanda.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a karkashin Nuhu Ribadu ta gabatar da tuhume-tuhume 70 a kansa, wadanda suka hada da tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004 a lokacin yana babban Sufeto Janar na ‘yan sanda. Ya yi yarjejeniya da kotu a kan mayar da mafi yawan kadarorin da kudaden. An yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.
Mai shari’a Binta Nyako ta ce hukuncin da aka yanke masa ya nuna cewa Balogun ya kasance mai laifi na farko kuma ya nuna nadama. Kotun ta umarce shi da ya biya Naira 500,000 a kan kowanne daga cikin tuhume-tuhume takwas da suka kai Naira miliyan hudu.
Shari’ar tasa ta cika da wasan kwaikwayo. Daya daga cikin irin wadannan shi ne lokacin da ya fadi a kan kujerarsa a ranar 29 ga watan Yuni, 2005, a babbar kotun Abuja.
Tsohon shugaban ‘yan sandan, wanda ya amsa laifuka takwas daga cikin tuhume-tuhume 56 da suka shafe shi kai tsaye, an same shi da laifi kuma an yanke masa hukuncin watanni shida a kowanne daga cikin tuhume-tuhumen, wanda za su tafi a jere lokaci guda.
An sake shi ne a ranar 9 ga Fabrairu, 2006 bayan ya gama daurin da aka yi masa, a wani bangare na asibitin kasa na Abuja.
(DAILY TRUST)