Tsohon Kakakin Majalissar Wakilai a Jamhoriyar ta biyu Benjamin Chaha ya rasu
Chaha Dan asalin karamar hukumar Ukum dake jihar Benue an bayyana cewa, yayi fama da rashin lafiya kafin rasuwar shi a yau Laraba
.
Ya zama wakili a majalissar Dokokin kasar nan ne bayan ya lashe Zabe a inuwar jam’iyar NPN a zaben shekarar 1983.
An Kuma Zabe shi a matsayin Kakakin Majalissar na tsawon Zango biyu na Mulkin Tsohon shugaban kasa Shehu Shagari a shekarar 1983
Dan marigayin Justice Steven Chaha ne ya tabbatar da mutuwarsa, sai dai ya bukaci wakilin Jaridar Punch daya dakata zuwa Gobe domin samun cikakken labarin
Yayin da aka tambayeshi shin ko Mahaifinja ya rasu sai Steven ya ce, ” Tabbas ya rasu, Amma Dan Allah kasameni a Ofishina gobe Alhamis, domin Jin cikakken rahoton”
An dai haifi Tsohon Kakakin majalissar ne a shekarar 1940.