Ministan karafa na jamhuriya ta biyu Wantaregh Paul Unongo ya rasu. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Unongo ya rasu ne a ranar Talata da yamma yana da shekaru 87 a duniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Harbe Shugabar Matan Jam’iyyar Labour LP A Jihar Kaduna
Dattijon ya rasu ne a wani asibiti da ke garin Jos na jihar Filato.
Tsohon Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa NEF, ya sha fama da rashin lafiya a ‘yan kwanakin nan kafin rasuwarsa.
An haifi marigayi Unongo a ranar 26 ga Satumbam shekarar 1935, kuma dan kabilar Kwaghngise-Anure- Abera ne a garin Turan na karamar hukumar Kwande a jihar Benue.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Zamfara Ta Gargadi Jam’iyyar PDP Akan ‘Yan Bangar Siyasa
Gwamnatin jihar Zamfara ta gargadi jam’iyyar hamayya ta PDP da kar ta sa ‘yan bangar siyasa a matsayin dabarun da za ta bi domin ganin ta ci zabe a jihar.
A zantawarsa da manema labarai mataimakin gwamnan jihar, Sanata Mohammed Nasiha, a gidan gwamnatin Gusau, ya zargi jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na gwamna da yin amfani da ‘yan barandan siyasa wajen kaddamar da hare-hare kan allunan talla da kadarori na ‘yan jihar da ba su ji ba ba su gani ba.