By Abbas Yakubu Yaura
Cif Ernest Shonekan, tsohon shugaban gwamnatin rikon kwarya da ya gaji mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida ya rasu.
Shonekan, malami ne a dakin taro kafin a zabe shi a matsayin shugaban rikon kwarya na kasa, ya rasu ne a Legas yana da shekaru 85 aduniya, kamar yadda TVC ta rawaito.
Ya kasance shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasa tsakanin ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwambar shekarar 1993 lokacin da aka hambarar da shi a juyin mulki a fadar sa karkashin jagorancin marigayi Janar Sani Abacha wanda shine sakataren tsaro na wancan lokacin.