Dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ba zai taka leda ba na tsawon watanni uku, sakamakon tiyatar da aka yi masa a kumatu da kuma idon sa.
Shugabannin kungiyar Kwallon kafa ta Napoli sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a shafinsu na intanet a ranar Talata.
Hakan na nuna cewa, Dan wasan ba zai buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Kamaru a shekara ta 2022 ba.
Sanarwar ta ce, “A safiyar ranar Talata, Gianpaolo Tartaro ne ya yi wa Victor Osimhen tiyata a kunci da kuma idonsa, wanda Dokta Mario Santagata ya taimaka tare da Dr Raffaele Canonico shi ma ya halarta.”
“Ana sa ran Osimhen zai dawo taka leda nan da watanni uku.” Inji sanarwar.
Dan wasan na Najeriya ya ji rauni ne a wasan da Napoli ta sha kashi a hannun Inter Milan da ci 3-2 a San Siro bayan sun yi karo da dan wasan bayan Inter Milan Skriniar ranar Lahadi.
Dan wasan mai shekaru 22 ya kasance dan wasan gaba na farko a Najeriya tun shekarar 2019 bayan da Odion Ighalo ya yi ritaya. Ya kasance cikin yanayi mai kyau ga tawagar kasar inda ya zura kwallaye hudu a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta Qatar na shekarar 2022 a Rukunin C.