Wani dan majalisar dokokin jihar Filato, Henry Longs ya rasu.
PUNCH ta tattaro cewa Longs, wanda ya wakilci mazabar Pankshin ta Kudu a karkashin jam’iyyar APC ya rasu ne a Jos a yammacin jiya Lahadi bayan da aka yi masa tiyata.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Philip Dasun, ya tabbatar wa da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya rasuwar Longs a ranar Lahadi.
Dasun ya ce, “Gaskiya mun rasa daya daga cikin mambobinmu da yammacin yau. Dan majalisa mai wakiltar mazabar Pankshin ta Kudu, Henry Longs.”
“Ya samu matsala a kafarsa daya kuma ya tafi aikin tiyata. Abin takaici, Mutuwar tasa ta yi matukar girgizamu, kuma za mu yi kewarsa.” inji shi.