Akalla mutum guda ne ya rasu a wani gini da ya ruguzo da sanyin safiyar ranar Asabar a karamar hukumar Birniwa ta jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:47 na asubahin wannan ranar ta Asabar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Jami’in ya ce wanda abin ya shafa ya mutu nan take yayin da wasu suka samu raunuka.
Ya ce jami’an ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya afku tare da kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Birniwa domin a duba lafiyarsu kuma a nan ne aka tabbatar da mutuwar mutane bakwai.
Karanta kuma: An Fara Zakulo Mutanen Da Suka Mutu Sanadiyyar Rushewar Gini
Adam ya ce ‘yan sandan ba su yi zargin wani ba saboda ginin da ya ruguje an gina shi ne da laka.
Kakakin, wanda a baya ya ce mutane bakwai ne suka mutu nan take, yayin da mutum daya ya samu rauni, daga baya ya kira wakilinmu ya tabbatar da cewa mutum daya ne aka tabbatar da mutuwarsa, ya kara da cewa sauran mutane shidan da ake tunanin sun mutu sun kasance a sume ne kawai, kuma a halin yanzu suna karbar magani.
Ya ce jami’an ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru tare da kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Birniwa domin a duba lafiyar su.
A wani labarin makamancin haka, an ceto mutane 10 daga kifewar kwale-kwale a karamar hukumar Kafin Hausa.
Rahotanni sun ce kwale-kwalen ya kife ne a tsakanin kauyukan Tage da Tafa na karamar hukumar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, al’amuran hatsarin kwale-kwale sun kasance a jihar a cikin makonnin da suka gabata inda aka samu hatsari har biyar wadanda suka yi sanadin mutuwar mutane akalla 19.
A wani labarin kuma: An Fallasa Daruruwan Makarantun Bogi Don Ciyar Da Dalibai
Akalla makarantun bogi 349 da aka yi rajistar shirin ciyar da yara a jihar Nasarawa ne tawagar kwamitin gwamnatin tarayya ta fallasa.
Shugaban tawagar kwamitin kuma mai ba wa Ministan Agaji, Malam Abdullahi Usman shawara, ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar ‘yan kungiyar zuwa gidan gwamnati dake Lafiya, domin kai ziyarar ban girma ga gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.