An kona wani jirgin kasa da ake amfani da shi wurin jigilar fasinjoji da kayayyaki a jihar Kwara.
Jami’ai biyu, daga cikin 15 na jirgin suna daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, wanda ya faru a karamar hukumar Offa a jihar, a yau Laraba.
Shaidun ga ni da ido sun bayya na cewa, wani mutum ne ya aikata wannan aika -aikar yayin da wutar ta tashi.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Shugaban sashin Hukumar kashe gobara na yankin a jihar Hakeem Adekunle, ya ce, masu kashe gobara sun shawo kan ba wutar.
A cewarsa, jirgin ya lalace ne, kuma ana kan gyara shi ne, lokacin da wani da ba a san ko wanene ba, ya banka masa wuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: A karon Farko WHO ta amince da Rigakafin Zazzabin Cizon sauro
“Mun Sami rahoton cewa, mutumin ya yi hakan da gangan ne. Amma, mun sami damar kashe wutar tare da kubutar da jirgin, bayan da biyu daga cikin jami’an jirgin suka kone. ”inji shi.
“Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa (CFO) ya bukaci jama’a da kada su yi jinkirin kiran hukumar kashe gobara a kan lokaci, a duk lokacin da aka samu wani lamari na gaggawa a yankunan su, domin hakan zai ceci rayuka da dukiyoyin mutane a cikin. jihar ”. A cewar shi.
Comments 1