Wasu sojojin da ba a san ko su wanene ba, sun kewaye gidan Firaminista Abdallah Hamdok na kasar Sudan, da sanyin safiyar yau Litinin, kamar yadda gidan talabijin na Al Hadath ya ruwaito.
Gidan Talbijin din ya ambato wasu majiyoyi da ba a san ko su waye ba, sun yiwa gidan Faraministan Diran Mikiya a Safiyar Yau Litinin.
Sai dai har kawo hada wannan rahoto Babu tabbacin abun da hakan ke nufi ga Faraministan na Sudan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi Awon gaba da Masu Ibada a Ogun
Dakarun soji sun Kuma kai farmaki gidan Mai baiwa Faraministan Shawara kan harkokin yada labarai, inda suka cafke shi da sanyin safiyar yau Litinin din, kamar yadda majiyoyin dangin Mutumin suka shaida wa Kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A wani labarin Kuma na daban.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta tsare tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim, dangane da binciken da ake yi kan tsohuwar Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Stella Oduah.
An gano dai cewa hukumar ta tasa keyar Anyim, a jiya Lahadi, inda ta tsare shi na awanni da dama dangane da wani asusun wanda aka gano wani kamfani da ya taba kasance darakta a Ma’aikatar.
An rahoto cewa ya isa ofishin EFCC da ranar Lahadi, kuma an yi masa tambayoyi sama da awanni shida.
Harkawo hada wannan rahoton bayanai sun nuna ce Anyim na tsare a tundaga jiya Lahadi, har zuwa hada wanann rahoton a yau Litinin.
Tsare tsohon SGF na zuwa kwanaki kadan bayan an ambaci sunan Oduah a cikin takardun Rahoton “Pandora Papers” a matsayin daya daga cikin ‘yan Nigeria 10 da ke boye dukiyarsu a wuraren da ake biyan haraji.
An yi imanin EFCC ta fara binciken Oduah da wasu da aka ambata a cikin rahoton.
Wata majiya ta ce, “Gayyatar Anyim da tambayoyi na da nasaba da shari’ar safarar kudi da ta shafi tsohuwar Ministan Sufurin Jiragen Sama kuma Sanata Stella Oduah.”Bincike ya nuna cewa, wani bangare na Kudaden ma’aikatar sufurin jiragen sama sun bace bat, inda aka Gano naira miliyan 780 a cikin kamfanin da Anyim ya taba jagoranta. ”
Daraktan yada Labarai da na EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya ce, ba shi da wani bayani kan tsare Anyim.