A halin yanzu ofishin ‘yan sanda na Ajali da ke karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar Anambra yana ci da wuta.
Haryanzu babu wani cikakken bayanai kan wanna lamari, amma Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kona Ofishin yan sandan ne sannan Kuma suka kashe wani jami’in.
A kwai Karin bayani….
A wani labarin na daban…
Sama da masu baiwa yan bindiga bayanan sirri guda 2000 ne aka kama a jihar Zamfara, sakamakon katse kafofin sadarwar da aka yi a jihar, a cewar Alhaji Ibrahim Dosara, Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai, Al’adu da yawon bude ido na jihar.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a jihar Kaduna a yau Alhamis yayin da yake ba da bayanai kan ayyukan soji da ke gudana a jihar.
Ya ce wadanda ake zargi masu ba da bayanai suna fuskantar tambayoyi ne a halin yanzu, domin su bayyana wadanda suke aikata laifin, da kuma abokan aikin su.
A cewarsa, wasu daga cikin wadanda aka kama sun ambaci sunayen manyan mutane a matsayin abokan hadin gwiwar su wurin gudanar da aiyukan ta’addanci a jihar.
Ya Kara da cewa, hukumomin tsaro suna aiki kan bayanan da wadanda ake zargin suka bada, don kamo wadancan abokan aikin na su.
Dosara ya ce jami’an tsaro da ke aiki dukkannin fadin jihar sun kashe yan bindiga da yawa yayin da da yawa suka tsere zuwa makwabtan jihohi kamar Sokoto da Katsina.
Kazalika ya ce, “Kwana daya da ta gabata, Kwamishinan rundunar yan sanda a Sokoto ya ce, kashi 80 na barayin Zamfara yanzu suna Sokoto, yayin da kashi 20 kacal suka rage a Katsina da Zamfara. Kamar yadda a yanzu hukumomin tsaro suka cafke sama da mutane 2000 masu bai wa yan bindigan a jihar bayanan sirri, kuma suna fuskantar tambayoyi kuma sun ambaci sunayen abokan aikin nasu, don hada wasu manyan mutane ne, kuma hukumomin tsaro suna aiki kan bayanan da aka bayar don samun abokan aikin su, ”in ji shi.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana sane da irin wahalar da aka shiga a jihar, na rufe layukan.inda Kuma yace, an yi hakan ne don kubutar da jihar daga hannun yan bindiga.
A karshe Kwamishinan ya ce, za a bude kafofin sadarwa a Gusau, babban birnin jihar kafin karshen wannan makon.
Comments 1