Yan bindigan da ake zargin sun yi garkuwa da Mai Martaba Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu, sun bukaci a biya su naira Milliyan dari biyu a matsayin kudin fansa, kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito
Daya daga cikin Fadawan Masarautar ta Kajuru ne, ya bayyana hakan a yau Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnonin Arewa na Jimamin Mutuwar Bala Bantex
Idan za’a iya tuna wa dai, da sanyin safiyar jiya Lahadi ce, yan bindigan su ka yi awon gaba da Sarkin, tare da Iyalan shi, da kuma wasu al’umar garin,