Wasu da ake kautata zaton Yan bindiga ne, sun farmaki garin Tsayau dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina, inda su ka kashe akalla Mutane 4.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewar, lamarin ya afku ne a jiya Litinin, inda yan bindigan suka afka garin tare da yin harbe-haben kan Mai uwa da wabi, kuma nan take suka kashe Mutum hudu, suka kuma yi awan gaba da wasu da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindigan da Suka Sace Dalibai a Zamfara sun bukaci Milliyan 350
Dan majalissan dokokin jihar Katsina Mai wakiltar yankin Jibia Mustapha Yusuf, ya tabbatar da faruwan lamarin, inda ya ce, harin ya kuma yi sanadiyar jikkata wasu mutane da dama.
A wani Labarin Kuma na daban.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranan Alhamis zai gana da shuwagabannin tsaro a Fadar Shugaban Kasa dake Aso Rock villa Abuja.
Babban Mai bawa Shugaban Kasa Shawara kan Kafofin Watsa Labarai da wayar da kan jama’a Femi Adesina, a ranar 17, ga watan Ogustan Shekarar 2021.
Shugaban Kasar wanda ya dawo birnin Abuja a ranan juma’a data gabata, bayan shafe kwanaki goma sha takwas 18 a birnin Landan, inda ya halarci wani taro kan ilimi tare da duba lafiyar sa.
Majiyar Jaridar Dimokradiyya ta gano cewa, Hukumomin tsaro cikin makonni hudu da suka gabata, sun kara kaimi sosai wurin yaki da masu tayar da kayar baya, da yan fashin daji, da sauran dukkanin masu aikata laifuka a kasar nan, kuma yanzu haka suke ta mika wuya dayawan su.
A lokacin taron, za’a gabatar wa Shugaban kasa cigaban da aka samu, tare da tsare-tsaren kawo karshen kalubalen matsaloli tsaro.