Yan bindiga sun afka yankin Katsit da ke karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna, inda akalla mutun uku ne suka sami raunuka sanadiyar harin.
Jaridar Daily Trust ta ce, Akalla mutun uku ne suka sami mummunan raunika a harin da aka kai yanki, a daran jiya Lahadi.
Kana DailY trust ta ruwai to cewa, Yan bindigan na shiga yankin suka fara harbi Kan mai-uwa da wabi.
Wani matukin babur din haya da ya tsallake rijiya da baya, ya bayyana wa Jaridar cewa, ” Na ga yan bindigan nazuwa ta bangaren gidan burodin dake yankin, inda suka tunkari sannanniyar kasuwar da ake saida Aladu dake yankin” a cewar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Manjo Yahaya tace Sojoji karda su ragawa Yan bindiga
Yankin na Katsit dake karamar hukumar Zangon kataf, ya yi magwaftaka da garin Kafanchan shelkwatar karamar hukumar Jama’a dake jihar Kaduna.
Harin na zuwa ne awanni kadan, bayan wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Malaman jinya, da jarirai a wani asibiti dake Zaria a jihar ta Kaduna.