‘Yan bindiga sun kashe mutane 17 a wani masallaci, yayin da suka Kai wani hari da sanyin safiyar yau Litinin a kauyen Maza Kuka da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.
An kuma yi garkuwa da wasu mutane 18 yayin harin na yau Litinin.
‘Yan bindigar sun mamaye unguwar ne a kan babura, yayin da mazauna garin ke yin sallar asuba, inda suka rika harbi ba kaukautawa
Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun harbe wasu wadanda abin ya rutsa da su, inda suka kashe mutane 17.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Kaddamar da Kudin E-Naira
Wasu daga cikin mazauna garin sun shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya a wayar salula cewa, har yanzu suna cikin Fargaban sanadiyar harin, wanda suka c,e ya ba su mamaki.
Al’ummomin Maza_Kuka da Kulhu da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja suna iyaka da dajin Kianji, inda aka ce mafi yawan ‘yan ta’addan suna fakewa a can.
Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya tabbatar da harin ga manema labarai.
Inda ya ce, an kashe mutane 16 a masallacin, yayin da wasu suka kashe daya a kauyen Kaboji.
Matane ya ce gwamnatin jihar ta tura wata tawagar sojoji zuwa dajin, don farautar ‘yan fashi da ke buya a can.
Kazalika Shugaban karamar hukumar Mashegu, Alhaji Alhassan Isa Maza-Kuka shi ma ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici ga mutane jihar baki daya.
A wani labarin Kuma na daban .
Al’ummar Tuomo, mai masaukin baki na Kamfanin Agip Oil na Najeriya, NAOC, a ƙaramar hukumar Burutu ta jihar Delta, ta rufe gidan mai da iskar gas saboda saba yarjejeniya da gaza samar da abubuwan buƙatu ga al’ummar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Al’ummar yankin, da suka hada da maza da mata, matasa da tsofaffi, dauke da kwalayen rubutu, sun yi tururuwa tare da kewaye cibiyar a yayin gudanar da zanga -zangar,a ranar Litinin, suna rera wakokin yaki tare da yin kira ga hukumar NAOC da ta yi abin daya dace.
Masu zanga zangar sunyi wasu rubuce-rubuce a cikin allunan wanda ke cewa “mun ce a’a ga Agip, ya isa ya isa, Agip, ta ba da haskenmu, babu haske babu aiki, al’ummar Tuomo ba za su bar Agip ya yi aiki ba har sai mun sami haskenmu, sai wata rana Agip da sauransu. .
Shugaban al’ummar Tuomo, Mista Tomke Binebai, wanda ya jagoranci zanga -zangar, yace: “Mutanen Tuomo sun yanke shawara a kan Agip kuma za mu ci gaba da zama har sai an biya buƙatun mu.
“Agip yana yi mana alƙawarin da yaudarar mu tun lokacin da suke aiki a nan a cikin shekarar 2009, sun yi alkawarin samar da haske ga Tuomo a matsayin mai masaukin su. Idan kun je tashar su, akwai wadataccen wutar lantarki amma jama’ar da ke karbar bakuncin su, suna cikin duhu.
“wannan cin mutunci da abin kunya ya isa haka, mun yanke shawarar mu kuma idan da gaske suna son yin aiki anan, su haskaka Tuomo, sannan su biya mana bukatun mu,da ɗaukar matasan mu aiki da GMOU.
Comments 1