A kalla mutane 7 ne yan bindiga suka harbe har lahira a wani kauye dake jihar Katsina.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, an Kai harin da musalin karfe 11:30 na daren jiya Alhamis, a kauyen Dan-kumeji dake karamar hukumar kankara na jihar ta Katsina, inda yan bindigan suka fara harbi kan mai uwa da wabi kan al’umar kauyen.
Kazalika a yunkurin mazauna kauyen na tsere wa, daga harin yan bindigan, sai suka afka wani kwantan bauna na yan bindigan da suka bude musu wuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: An kashe Fararan hula 210 a Habasha
Bayan wadanda suka mutu sanadiyar harin, mutane 6 sun sami mummunan raunika kuma ankai su asibiti domin duba lafiyar su.
“Lokacin da mutanan mu suka gansu, sai su k ayi kokarin tsere wa cikin daji, ashe wasu daga cikin yan bindigan na labe a dajin, inda suka fara harbin su” inji wani mazaunin yankin mai suna Abdulmiminu Sani da yake zantawa da Jaridar Daily Trust ta wayar Salula.
Har’ilayau yace, tuni aka fara shirye-shiryen birne gawar-wakin wadanda harin ya rutsa da su.
Har’izuwa hada wannan rahoton, rundunar yan sandan jihar Katsina, ba ta ce komai ba kan wannan lamari.