Akalla masu ibada 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da aka kai a wani masallaci a kauyen Ba’are da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.
Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a lokacin da mutanen kauyen ke gudanar da sallar asuba.
Wata majiya ta ce an kai wadanda suka samu raunuka zuwa babban asibitin Kontagora domin yi musu magani.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryas, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce akalla mutane 9 ne suka mutu a harin.
“Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta riga ta tura jami’an tsaro zuwa yankin da abin ya shafa domin kara kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” inji shi.
Ya jaddada cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar da ‘yan Najeriya tare da yin kira da a samu sahihin bayanan sirri daga jama’a.
Harin dai na zuwa ne kasa da watanni biyu bayan da wasu ‘yan bindiga suka bindige wasu masallata 18 a wani masallaci da ke karamar hukumar.
An kai harin ne a kauyen Mazakuka da ke karamar hukumar Mashegu a ranar 26 ga Oktoba shekarar 2021.
Allakawo manaxaman lpy