‘yan bindiga a karkashin jagorancin shugabansu Turji, sun kai hari a babbar kasuwar garin Goronyo ta jihar Sakkwato.
‘Yan bindigar wanda ganau suka ce sun fi dari, sun kai hari a kasuwar ne da yammacin jiya Lahadi da misalin karfe 4:50 na yamma, a daidai lokacin da mutanen kauyakun ke saye da sayarwa a kasuwar, inda suka bude musu wuta.
Majiyarmu ta labarto mana cewa; ‘yan bindigar sun kwashe fiye da awa biyu ba tare da sun fuskanci wata turjiya daga hukumomin tsaro ba sakamakon babu hanyar da za a sanar da su saboda katse sadarwa da aka yi a yankin.
A cewar majiyarmu, akalla gawarwaki 40 aka kirga a daren ranar Lahadi.
Bayanai daga wadansu mazauna garin na Goronyo, sun tabbatarwa da majiyarmu ta jaridar DailyStar cewa akalla ya zuwa yanzu gawarwaki 62 aka ajiye a babban asibitin Gwamnati na Goronyo ya zuwa safiyar yau Litinin. Banda wadanda ‘yan’uwa suka dauki gawarwakin ‘yan’uwansu domin yi musu jana’iza.
Kuma bayanai sun tabbatar da cewa da yawa sun bace har yanzu ba a gan su, a yayin da ake tsammaninsu wasu sun shige daji ne sakamakon gujewa harbe-harben ‘yan bindigar.
Sannan rahotanni sun ce an jikkata da dama wanda a halin yanzu wasu ke karbar magani a asibitin. Wasu kuma sun samu matsalar kwakwalwa sakamakon dimaucewa daga harin ‘yan bindigar.
Ya zuwa hada rahoton nan, duk yunkurin da muka yi domin jin ta bakin Kakakin ‘yan sandan jihar Sokoto, abin ya ci tura.
Kasuwar Goronyo dai babbar kasuwa ce ta albasa da shanu.