• Yan bindiga sun kashe wani Janar din soji, a hanyar Abuja zuwa Lokoja
• Bayan kashe jami’in Yan bindigan sun yi garkuwa da matar shi a jiya Alhamis.
• Rundunar sojin ta ce, za’a yi jana’izar Marigayin ne a yau juma’a da musalin karfe goma a Abuja.
Rundunar sojin kasa ta kasar nan, ta tabbtmatar da kashe wani babban jami’in ta, Mai suna Major Janar Hassan Ahmed, lokacin da mahara suka farmake shi a babban hanyar Lokoja zuwa Abuja.
Jami’in Hulda da jama’a na rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau juma’a, inda ya ce, za’ayi jana’izar Marigayin ne a yau juma’a 16 ga watan Yuli shekarar nan, a makabartar Barikin Lungu dake Abuja, tare da cikakken girmamawar rundunar soji.
Kazalika a lokacin da yan bindigan suka kai ma babban jami’in hari, sun yi garkuwa da matar shi, a cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar.
Ya kuma ce,” Tare da karfin zuciya Babban Hafsan sojin kasar kasar nan, Laftanar janar Faruk Yahaya da manyan jami’an soji, da kuma sauran jami’an rundunar, na takaicin sanar da al’uma mutuwar Manjo Janar Hassan Ahmed Tsohon Shugaban Makarantar Soji ta kasa.” Inji jami’in.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin tarayya ta bai wa Jihar Yobe kyauatan Motocin Kashe Gobara
” Lamarin ya afku da bababn jami’in sojin ne, lokacin da yan bindiga suka farmaki motar shi dake kan hanyar Lokoja zuwa Abuja a jiya Alhamis, 15 ga watan Yulin Shekarar 2021.” Inji shi.
“An tura da wakilan jami’an daga rundunar soji, wanda Shugaban sashin tsare-tsaren Manjo Janar Anthony Omozoje ya jagoranta, domin ziyartar Yan uwa da abokan arzikin wadanda lamarin ya shafa.” Inji jami’in.
Kazalika a cewar shi, “Mambobin kungiyar matan jami’an sojin ta kasa NAOWA, kar kashin jagorancin Mataimakiyar Shugaban kungiyar ta kasa Mrs Stella Omozoje sun ziyarci iyalan Mamacin, domin jajanta musu.
A karshe ya ce, Ana kara tunatar da mutane cewa, “Za’ayi Jana’izar babban jami’in ne a makabartar Barikin Lungu a yau juma’a, 16 ga watan Yulin Shekarar 2021, da musalin karfe 10 na safen Nan” inji shi.