By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun shiga wani asibiti a Yola babban birnin jihar Adamawa a yammacin ranar Litinin, inda suka yi awon gaba da mamallakin Asibitin.
Wanda lamarin ya shafa, Dokta Saidu Bala, shi ne tsohon Darakta na asibitin kwararru na Yola.
Wata majiya tace ‘yan bindigar sun mamaye asibitin ne bayan karfe 6 na yamma, a daidai lokacin da mazauna unguwar suke yin sallar Magariba.
Majiyar tace nan da nan suka isa asibiti, sai suka yi ta harbe-harbe don tsoratar da mutane.
‘Yan bindigar sun kai farmaki asibitin jim kadan bayan sallar Maghrib inda suka yi harbin akan iska don tsoratar da mutanen dake ciki da kuma wajen Asibitin.”
“Sai suka je ofishin Dakta Saidu Bala suka tafi da shi. An gudanar da aikin cikin gaggawa cikin kasa da mintuna biyar,” majiyar ta shaida wa wakilinmu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar wa da Jaridar Aminiya faruwar lamarin, inda yace an tura jami’ai domin zakulo maharan tare da kubutar da wanda aka sace.
“Mutanenmu sun gano tulun harsashi guda uku da aka yi amfani da su a wurin da laifin ya faru, kuma nan take mun tura jami’an yaki da garkuwa da mutane domin ceto likitan da aka sace,” inji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da ake fargabar yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a kasar, musamman a arewacin kasar.