Wasu yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba sun kutsa kauyen Unguwar Kabulo dake karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna inda suka yi awun gaba da mutane 14.
Wani mazaunin kauyen ya shaida cewa yan bindigar tun da farko sun kwashe mutane 17 ne, amma daga bisani 3 daga cikin su sun tsallake rijiya da baya bayan da suka kubuta daga hannun yan bindigar.
Wani Makwabcin kauyen mai suna Muhammad ya ce yan bindigar sun shiga kauyen wuraren karfe daya na rana a yau Lahadi inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar ASP Muhammad Jalige Dangane da lamarin, ya ce a bashi lokaci don gudanar da bincike kan gaskiyarsa.