Yan bindiga sun kai hari wani kauye a karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto, inda suka kashe mutane shida.
Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, yan bindigan sun mamaye kauyen ne da sanyin safiyar yau Lahadi, wanda galibim mazauna garin mafarauta ne,
Kazalika rahotanni na nuna cewa, Harin na zuwa ne, bayan da yawancin mutanen garin suka fita farauta.
Sai dai Babu tabbas, ko harin yana da nasaba da kisan gungun yan bindiga 13, wadanda suka kai hari garin Tangaza a jiya Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Mutum 3 a Anambra
Amma Majiyarmu ta bayyana cewa, wasu matan aure guda biyu na cikin wadanda abin ya shafa, a kauyen na Saminaka dake jihar Sokoto.
“Sun harbe mata biyu har lahira kuma sun kashe samari hudu” inji wata majiya
Kazalika majiyar ta bayyana cewa, “Amma duk jami’an Yan Sakan garin sun bi sahun Yan bindigan cikin daji a halin yanzu.”
Idan za’a iya tunawa dai a jiya Asabar, wasu fusatattun mutane sun kashe tare da kone gawarwakin yan bindiga 13, wadanda suka kai hari, kuma suka kashe mutane hudu a garin Tangaza dake jihar Sokoto.