•Yan bindiga sun sake yin garkuwa da Mutum 13 a Kaduna
• Lamarin ya farune a jiya laraba a Unguwar Gimbiya dake Sabon Tasha.
• Hakan ya yi sanadiyar fitowar Matasa kan titi domin yin zanga-zanga.
An sake karkuwa da akalla Mutum goma sha uku, a Unguwar Gimbiya da ke yankin sabon Tasha na karamar hukumar Chikun, dake jihar Kaduna.
Lamarin ya afku ne da musalin karfe goma sha daya, na daren jiya Laraba.
Rahotanni sun nuna cewar, a kalla Mutum 6 ne, da suka hadar da Dillali da kuma Mazauna wani gidan haya akayi awan gaba dasu, sanadiyar harin na jiya da Yan bindiga sukai a yankin.
Hakan na zuwa ne kasa da awanni 48 da garkuwa da daliban Makarantar Bethel Baptist guda 120, a garin Maraban Rido dake a karamar hukumar ta Chikun, a ranar Litinin din da ta gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cuta Kwalara ta kashe Mutun 14 a jihar Filato
Kazalika hakan yayi sanadiyar, fusata wasu Matasa dake yankin, inda suka fito zanga-zanga, Kuma suka toshe babban haryar Sabon Tasha zuwa garin Kachia, da safiyar yau Alhamis.
Masu zanga zangar sun toshe hanyar, Wanda hakan ya kawo cinkoson ababen hawa a kan babban hanyar.
Sai dai ya zuwa hada wannan rahoton, duk yunkurin da jami’an tsaro su kayi na tarwatsa matasa masu zanga-zangar a kan hanyar abun ya citira.