Shugaban jam’iya Mai Mulki ta APC a Yankin Arewacin jihar Niger Alhaji Aminu Bobi, ya shaki iskar yanci daga hannun masu Garkuwa da mutane.
A dai makon da ya gabata ne, wasu da ke kyautata zaton ma su garkuwa da mutane ne, su ka je har gonar shi dake kan hanyar Ukuru na Masarautar Bobi, dake karamar hukumar Mariga na jihar su ka yi awon gaba da shi.
Sai dai har yanzu jaridar Dimokuradiyya na da kon cikakkun bayanai kan sakin Alhaji Aminu Bobi da yan bindigar su kayi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyan Ruwa Buhari ya jajanta wa takwararnshi na Jamhoriyar Niger
Indan ba’a manta ba dai jihar Niger, na daya daga cikin jihohin da Yan bindiga ke addaba su a Nigeria, musamman ma a yan kwanakin baya bayan nan.
A kwai Karin bayani….
A wani labarin na daban…
Babbar Kotun Tarayya dake zaman ta a Port Harcourt, Jahar Rivers ta zartarwa Morgan Chinda da akafi sani da Richard Johnson Adams, tare da Joshua Pina hukuncin daurin Shekaru uku a gidan yari, sakamakon kama su da laifin Damfara a yanar gizo.
Wadanda aka tura gidan Yarin, an yanke masu hukuncin ne a dalilin Sojan gona da kuma Damfara, inda Hukumar Kula da hana Zagon Kasa da Almundana ta shiyyar Port Harcourt ta kama, ta kawo su gaban Mai Shari’a A.T. Mohammed.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kula da Kafafen Yada Labaru na EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar ga Manema Labaru a Port Harcourt.
Bayan an kamasu da laifi dumu-dumu, Mai Shari’a Mohammed ya zartarwa Morgan Chinda hukuncin gidan yari na tsawon Shekaru biyu ko kuma biyan tara ta Naira 250,000, a yayinda Pina aka yanke mashi hukuncin gidan yari na tsawon Shekara Daya ko kuma biyan tara ta Naira 50,000.
Babban Jojin ya bada umarnin kwace Wayoyin da aka samu a wurin su, a lokacin da za’a kamasu , da suka hada da; iPhone 6S da iPhone 6 gami da Qukitel C 19 ga Gwamnatin Tarayya.
Comments 1