Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Charles Mato Dakat, babban basaraken garin Gindiri da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Jaridar Daily Trsut ta ruwaito cewa an yi garkuwa da basaraken ne bayan an yi ta harbe-harbe a gidansa da sanyin safiyar Lahadi.
Manjo Ishaku Takwa, kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ (OPSH), da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce an tura jami’an sojoji zuwa yankin kuma suna nan ana bin sahun masu garkuwa da mutane.